Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Farfesa Amina Salihi Bayero, a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar Northwest.
Naɗin nata zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamban 2025, har zuwa tsawon shekaru biyar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar, ta ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan tantancewa da kwamitin gudanarwar jami’ar ya yi mata.
A matsayinsa na jagoran jami’ar, Gwamna Abba, ya yaba wa shugaban kwamitin da mambobinsa kan jajircewarsu wajen bin ƙa’idojin tantancewar.
Haka kuma ya nemi a yi mata addu’ar samun nasara wajen gudanar da jagorancin Jami’ar.
- EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige
- An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a Indiya
Farfesa Amina Salihi Bayero ƙwararriya ce a fannin Chemistry, musamman Analytical Chemistry, kuma ita ce mace ta farko da ta samu digiri na uku a fannin daga Jami’ar Bayero Kano.
Ta taɓa riƙe muƙamai da dama a harkar ilimi da gudanarwa, ciki har da shugabar sashen Chemistry, da kuma Mataimakiyar Shugabar Jami’a (DVC) a Jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Ana girmama ta saboda jajircewarta wajen horar da matasan masana kimiyya.
Ana sa ran naɗin nata zai ƙara ɗaukaka martabar jami’ar, ya inganta tsarin ilimi, tare da bai wa mata ƙofar samun manyan muƙamai a Jihar Kano.
