Shugaba Tinubu Ya Nanata Kudurinsa Na Janye Yansanda

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nanata ƙudurinsa na janye ƴansanda daga gadin manyan mutane a ƙasar, inda ya ce janyewar ta zama tilas.

Ya ce babu gudu babu ja da baya a matakin da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga dukkan ministocin ƙasar su yi abin da ya dace ba tare da ɓata lokaci ba. Ya ce idan abun kuma ya zama dole to shi da kansa ne zai yi umarnin ba da ‘yansandan.

Tinubu ya bayyana haka ne a taron majalisar zantarwa na ƙasar, inda ya buƙaci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da ministan ƴansanda Ibrahim Geidam da shugaban ƴansanda Kayode Egebtokun su tabbatar an aiwatar da umarnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *