Gwamnan Kano ya naɗa Alhaji Sani Abdulkadir Dambo shugaban hukumar tattara haraji ta jiha

Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya naɗa Alhaji Sani Abdulkadir Dambo a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta jiha wato KIRS.

Hakan na ƙunsha ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga shafin Sakataren yada labaran Gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofainda ya bayyan cewar, shugaban na hukumar harajin, na cikin kungiyar malaman haraji na kasa, kuma ya fi shekara 20 ya na irin wannan aiki.

Kafin yanzu ya rike wannan mukami a baya, sannan yanzu haka Sani Abdulkadir Dambo babban jami’i mai binciken haraji ne a hukumar tattara haraji ta kasa. A yammacin Alhamis ne dai aka ji cewa, Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi ya zama sabon shugaban hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa. inda  Isyaku Abdullahi Kubarachi da Dambo za su fara aiki daga yau Juma’a, 16 ga watan Yuni 2023.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere

Yan sanda da INEC sun yaba da yadda zaɓen Dawakin Kudu ke gudana a Kano.