Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sake amincewa da Sabbin nada-naden sabbin mukamai a gwamnatinsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran gwamnan Kano Bature Dawakin Tofa ya aikowa muhasa.
Wadanda aka nada sun haɗa da:
Arc. Ahmad A. Yusuf a matsayin babban sakataren , maikatar tarihi da raya al’adu ta jahar kano.
Sai. Engr. Ado Jibrin Kankarofi, a matsayin mukaddashin manajan director, na hukumar kula da hanyoyi na jahar kano wato KARMA.
Sai kuma Hauwa Muhammad a matsayin mai bawa gwamana shawara na musamaman kan harkokin mata.
Sanarwar ta ce Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf wanda ake wa lakabi da Abba Gida-gida ya taya su murna tare da cewa nadin nasu ya fara aiki ne nan take.