Gwamnan KANO Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kudin jarrabawar NECO ga daliban makarantun gwamnati 55,000 domin samun damar rubuta jarabawar ta kammala makarantar sakandire ta shekarar 2023 (SSCE).
Gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 20 din farko da suka gabata a gwamnatinsa.
Abba Kabir Yusuf ya bukaci daliban da suka amfana da su yi aiki tukuru don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa, gwamnatinsa za ta cigaba da lalubo manufofi da tsare-tsare na inganta harkar ilimi, domin ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.