Home » Gwamnan Kano ya umarci muƙarrabansa su ajiye mukamansu a ranar 26 ga watan nan

Gwamnan Kano ya umarci muƙarrabansa su ajiye mukamansu a ranar 26 ga watan nan

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Gwamnan Kano ya umarci muƙarrabansa su ajiye mukamansu a ranar 26 ga watan nan

Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarni ga dukkanin Kwamishinoni da shugabannin Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin kano da su ajiye mukamansu nan da ranar juma’a 26 ga wannan wata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin Kano ya fitar mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ofishin Bilkisu Shehu Maimota.

Sanarwar ta kuma bukaci masu mukaman Siyasa da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan Sakatarorin gwamnatin ko daraktoci ma’aikatunsu tare da kayan gwamnati dake wurinsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa wadanda mukamin da aka ba su yana da wa’adin sauka to su cigaba da rike mukamansu dai-dai da yadda dokokin da suka nada su suka tanada.

Sanarwar ta godewa daukacin wadanda suka rike mukaman saboda irin gudunmawar da suka bai wa gwamnatin da kuma irin nasarorin da ta samu tsahon shekaru 8 da suka gabata.

Sanarwar ta ce ajiye mukaman ya hadar da kwamishinoni da masu bai wa gwamna shawara da mataimakan gwamna na musamman da manyan mataimaka na musamman ga gwamna da duk Masu rike da mukaman Siyasa.

A ranar Litinin 29 ga watan mayu za a rantsar da sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?