Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta kara farashin yin fasfo daga ranar day aga watan Satumbar 2025.
A cewar wata sanarwa da Kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce karin ya shafi iya wadanda suka nemi fasfo din a iya cikin Najeriya ne.
“A yanzu duk fasfo mai shafi 32 ya koma N100,000 wanda zai yi shekara biyar kafin ya daina aiki, yayin da mai shafi 64 da zai shekara 10 ya koma N200,000,” in ji sanarwar.
- An Kashe Mutane 3 A Faɗan Kungiyoyin Asiri A Legas
- Shugaba Tinubu Ya Koma Najeriya Bayan Ziyartar Japan Da Brazil
Sai dai sanarwar ta ce har yanzu kudaden da masu neman fasfo din daga kasashen waje ke biya na Dala 150 ga fasfo mai shafi 32 da Dala 230 a mai shafi 64, bai canza ba.
Hukumar dai ta ce an yi karin ne domin a inganta inganci da tsaron fasfo din sannan kuma ya ci gaba da samuwa ga ’yan kasa.
Yanzu haka dai kafin karin, ana biya N50,000 ga fasfo mai shafi 32, sai kuma N100,000 ga mai shafi 64.