Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin.
Shaidu sun ce ƙungiyoyin asirin biyu sun yi artabu da bindigogi, adduna da kwalabe.
Ɗan sandan da ya ji rauni an garzaya da shi asibiti, inda yake cikin mawuyacin hali.
Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
- Shugaba Tinubu Ya Koma Najeriya Bayan Ziyartar Japan Da Brazil
- Amurka Ta Daure Basaraken Osun Kan Zamba A Tallafin COVID-19
Amma ta ce komai ya daidaita tare da wanzar da zaman lafiya bayan da jami’an tsaro suka isa yankin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Olohundare Jimoh, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa kasuwar, inda suka buɗe hanyoyin da aka toshe yayin rikicin.
“A lokacin rikicin, mutane uku sun mutu a asibiti sakamakon raunukan da suka samu, yayin da wani ɗan sanda ɗaya ke cikin mawuyacin hali a asibiti,” in ji Hundeyin.
Rundunar ta kuma ƙaryata jita-jitar cewa rikicin ƙabilanci ne ya tashi a kasuwar Balogun.
Ta tabbatar da cewar faɗa ne tsakanin wasu ’yan daba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya, kuma ba shi da alaƙa da ƙabilanci.