Gwamnatin Tarayya ta rage harajin shigo da kayan abinci da magunguna da motoci da wasu kayayyaki daga ƙasashen waje.
Gwamnatin ta kuma soke biyan harajin shigo da wasu kayayyaki daga ƙasashen waje, bayan ta amince da aiwatar da sabbin manufofin kudi na shekarar 2026, wadanda suka kunshi sauye-sauyen haraji masu muhimmanci.
A cikin wata takarda da aka fitar ranar 1 ga Afrilu, 2026, mai dauke da sa hannun Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, gwamnati ta bayyana cewa sabbin matakan sun shafe na shekarar 2023.
Sabuwar manufar ta kunshi jerin kayayyaki 127 da aka rage musu kudin shigo da su, domin ƙarfafa ci-gaban muhimman sassa na tattalin arzikin ƙasa.
A cewar takardar, harajin shigo da motoci da aka kera gaba ɗaya, da motoci 4-wheel drive da station wagon yanzu an rage harajin shigo da su zuwa kashi 40 cikin 100, maimakon kashi 70 da aka kafa tun a shekarar 2015.
Harajin shigo da manja ya sauka zuwa kashi 28.75 cikin 100, daga tsohon tsarin da ya fi tsauri.
An kuma rage harajin shigo da shinkafa a daga kashi 70 zuwa kashi 30, amma shinkafa da ke cikin buhu mai nauyin kilo 5 zuwa an rage harajinta ne zuwa kashi 45.
Harajin shigo da sukari kuma an rage shi daga kashi 70 zuwa 55 -57.7 cikin 100.
An kuma rage harajin shigo da rodi da kwanan rufi da kayan lantarki da magunguna da kayan asibiti da kayan rubutu.
Gwamnati ta kuma bayar da wa’adin kwanaki 90 ga ’yan kasuwa da suka riga suka bude Form ‘M’ kafin 1 ga Afrilu, domin su shigo da kayansu bisa tsohon tsarin haraji.
Sai dai kuma, sabon tsarin harajin kaya (excise duty) da kuma harajin muhalli (green tax surcharge) za su fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026.

