Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Zayyanu A Salihu ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram.
Ya ce dokar ta tsawon sa’a 24 za ta soma aiki bayan sallar Juma’a.
Hukumomi sun shawarci jama’a da su mutunta dokar.