Gwamnatin Jihar Kano ta umarci yan kasuwar mangoro dake na’ibawa yanlemo dasu kauracewa yin bahaya a Wani kebantaccen fili dake bakin titi Kuma su daina sauke Kaya a kusa da wajen domin kaucewa kamuwa da cututtikan da iska kan Iya yadawa.
Kwamishinan ma’aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayin na Jihar Kano Dr. Dahiru Mohammad Hashim ne ya bada Umar nin lokacin da ya ziyarci fili domin gani da Ido, kwamishinan Wanda ya gayyaci shugabancin kasuwar ta Na’ibawa ya zagaya dasu Inda Kuma ya bayyana damuwarsa kan yadda yaga jama’a na yin bahaya a filin.
Ya Kuma bada umarnin kwashewa tare da share fili ya Kuma gargadesu da kada su sake yin bahaya a wannan waje.
Dr. Hashim ya sha alwashin ci gaba da kawo ziyara wannan waje domin tabbatar da anbi doka da oda tare da daina yin bahaya gaba daya a filin.
Kwamishinan ya Kuma ziyarci kasuwar yan Nono dake jikin tashar Kano line kan titin Zaria Inda Suma ya tattauna dasu tare da basu shawarar sake matsuguni ba kan babbar hanya ba don ci gaba da sana’oinsu ba tare da kawo Wani cikas ba kasan cewar wannan hanya mashiga ce ta Jihar Kano.
Haka zalika ya gayyace su suzo office domin tattaunawa dasu don cimma matsaya game da kasuwancin nasu. Kwamishinan yace burin gwamnatin ne ta samarwa da jama’a matsuguni na dumdumdin kuma wanda ya dace domin gudanar da sana’oinsu na yau da kullum.
Haka Kuma tawagar ta sake ziyartar kasuwar yan kifi dake kan titin BUK daura da ofishin yan Sanda na zone l, Inda nan ma aka basu Sati daya dasu tashi daga wannan waje kasan cewarsa yayi kan titi sosai Kuma bai dace da irin wannan Sana’arba, ya Kuma gayyace su suzo office domin tattaunawa kan yadda Za a Samar musu da Sabon matsuguni don ci gaba da sana’oinsu na yau da kullum.
“Daga bisani ya sake jaddada kudirin gwamnatin Kano naci gaba da bunkasa harkar kasuwanci a jihar Kano ta hanyar da ya dace ba tare da an gurbata Muhalli ba Ko haifar da yaduwar cututtuka, inji Kwamishinan “.
Yayin wannan rangadi kwamishinan yana tare da Manajan Dirakta na hukunar Karota Injiniya Faisal Mahmoud da Dirakta daga hukunar kula da hakkin Mai Saye da mai sayarwa ta Jihar Kano wato ( Kano State Consumer Protection Council) da sauran Diraktoci daga ma’aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayin ta Jihar Kano.