Yadda Shagon Rahama Sa’idu Ya Kama Da Wuta

Da safiyar jiya Laraba ne dai aka ga jarumar tiktok Rahama Sa’idu na bayyana cewa an karya mata allon da ke gaban shagonta, kuma ta sha alwashin sai an biyata. 

Yayin da daga bisani kuma shugaban hukumar karɓar korafe-korafe na Kano Barista  Muhyi Magaji ya titsiye ma’aikatan KNUPDA saboda cire allon shagon Jarumar.

A wani faifayin bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado na bin bahasin yadda Hukumar KNUPDA ta cirewa Rahma Allon tallantan shagonta.

Inda a yammacin ranar Alhamis rahotanni suka tabbatar da cewa hukumar KNUPDA ta je ta rushe duk wata rumfa da ke gaban shagunan inda shafin Rahama ya ke, ciki har da nata.

Kafin daga bisani kuma a cikin daren Alhamis ɗin nan aka ce shagon jarumar ya kama da wuta. Kawo yanzu babu wani bayani daga hukumomi da kuma jarumar kan gobarar da ke ciki a dai-dai lokacin haɗa wannan rahoto.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *