Gwamnatin Jihar Kano Ta Sanya Dokar Zaman Gida na Awa 24

Gwamnatin jihar Kano, ta bakin kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba, ta sanar da sanya dokar zama a gida na daga safiyar wannan rana zuwa dare.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen gwamna na jihar Kano da hukumar zaɓe ta yi tare ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ya ce wannan mataki ne da aka  ɗauka domin magance yiwuwar ɓarkewar tashe-tashen hankula a jihar.

Sai dai har izuwa yanzu al’umma na cigaba da fitowa da yawo kan tituna domin bayyana farin cikinsu game da nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr