• Home  
  • Gwamnatin jihar Kano tasha alwashin magance matsalar ruwan sha.
- Babban Labari

Gwamnatin jihar Kano tasha alwashin magance matsalar ruwan sha.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, yasha alwashin kawo ƙarshen matsalar ruwan sha, a yayin wata ziyarar gani da ido da yakai matatar ruwa ta Tamburawa dake jihar. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mustapha Muhammad, ya fitar. A yayin rangadin, an gano matsaloli da suka haɗa […]

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, yasha alwashin kawo ƙarshen matsalar ruwan sha, a yayin wata ziyarar gani da ido da yakai matatar ruwa ta Tamburawa dake jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mustapha Muhammad, ya fitar.
A yayin rangadin, an gano matsaloli da suka haɗa da zubewar ruwa a bututu, lalacewar wasu injuna da kuma tsufan wasu kayayyaki, inda gwamnan ya yi alƙawarin daukar matakan gyara da sabunta wasu.
Da yake zantawa da manema labarai, Gwamna Abba ya jaddada ƙudurin gwamnatin sa na gyara cibiyoyin tace ruwa da inganta samar da ruwa ga al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnati za ta haɗa kai da kwararru daga kasar China domin tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta kuma wadatacce, yana mai cewa samar da ruwa mai kyau na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai