• Home  
  • Gwamnatin Kano Ta Bukaci Tallafin Daidaikun Mutane A Bangaren Ilimi
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Kano Ta Bukaci Tallafin Daidaikun Mutane A Bangaren Ilimi

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci ɗai-daikun jama’a da su riƙatallafawa a bangaren ilimi domin samun nasara a kokarin da takena magance matsalon da makarantun jihar ke ciki. Gwamantin ta bayyana hakan ne ta bakin kwamishinan tsaro daayyuka na musamman na jihar Air vice marshal Ibrahim Umar mairitaya wanda ya wakilici gwamannan Kano Alhaji Abba Kabir […]

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci ɗai-daikun jama’a da su riƙa
tallafawa a bangaren ilimi domin samun nasara a kokarin da take
na magance matsalon da makarantun jihar ke ciki.

Gwamantin ta bayyana hakan ne ta bakin kwamishinan tsaro da
ayyuka na musamman na jihar Air vice marshal Ibrahim Umar mai
ritaya wanda ya wakilici gwamannan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a
wajen ganin gyaran makarantar firamare ta kofar Na’isa da tsohon
dalibin makarantar ya yi.

A nashi bangaren babban darakta na ƙungiyar rajin kare ilimi da
dimukradiyya ta SEDSAC Kwamared Umar Hamisu Ƙofar Na’isa
ya yaba da wannan kokari na samar da ci gaba a fannin ilimi.

A ƙarshe an bukaci al’umma da su riƙa bibiyar halin da
makarantun da suka gama ke ciki domin bada gudunmawar da
zata amfani al’umma

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000