Gwamnatin jihar Kano ta daukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke cewa ta biya diyyar Naira Miliyan Dubu 30 ga wadanda ta rushewa shaguna a filin idi dake unguwar kofar mata.
Kotun ta yanke hukuncin biyan diyyar Naira Miliyan Dubu 30 din ne ga ‘yan kasuwar, maimakon Naira Miliyan Dubu 250 da suka nema daga gwamnati biyo bayan rusau da gwamnatin kano ta yi musu tun farkon hawanta mulki.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce ta daukaka kara kan hukuncin da ta bayyana a matsayin rashin adalci.
Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotu ba ta yi daidai ba wajen yanke hukuncin ga kungiyar ‘yan kasuwa saboda dokar amfani da filaye a kowace jiha.
A karshe ya ce kotun ba ta da hurumin ko da sauraren ƙarar saboda gwamnati ce kadai ta mallaki fili kamar yadda dokar amfani da filaye ta tanada.