A wani yunkuri na tabbatar da da’a tare da bin ka’idojin da dokar hukumar tace fina-finai ta samar kan hotuna da kalamai su zamo masu ma’ana, Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta sanar da haramta lika duk wani nau’in hoto ko kalmomi marasa ma’ana ajikin baburan Adaidaita Sahu a fadin Jahar Kano.
A cewarsa Jami’in yada labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan samun korafe korafen al’ummar jihar Kano dangane da yadda masu baburan adai-daita sahu ke nuna hotuna marasa ma’ana ko rubuce rubuce inda suke yawo a tituna batare da jin kunya ba.Abba El-mustapha ya ce dokar da ta kafa hukumar ce ta ba ta cikakken iko na sanya ido tare da hukunta masu irin wannan laifi.
- Mutane 366 Sun Mutu Sakamakon Zazzabin Lassa Da Sankarau: NCDC
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Dan Boko Haram Abu Fatima.
Cikin wani salo na tabbatar da bin wannan umarni, Abba El-mustapha ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin kai ziyara manyan titunan Jahar Kano Wanda suka hada da Maiduguri Road, Zariya Road, da Sani Marshal Road dan a wayar da kan al’umma musamman masu tuka baburan adai-daita sahu kan sabuwar dokar inda ya nanata cewa hukumar ba za ta sassauta ba wajen hukunta duk wani da aka samu da karya dokokin Hukumar ba komai matsayin sa.
Ya kara da cewa, bisa dokar hukumar, duk wani aiki na adabi ko na fasaha dole ne a turoshi gaban hukumar don tantancewa kafin a fitar da shi ga jama’a a saboda da haka ana bukatar al’umma su bada cikakken goyan baya da Kuma hadin Kai domin cigaban Jahar Kano.A baya baya idan ba’a manta Hukumar ta fita irin wannan aiki na gwaji domin wayar da kan al’umma musamman matuka baburan adai-daita sahu inda ta Sami sama da babura 20 tare da yi musu gargadi tafi sabuwar dokarta ta fara aiki.
