Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram wanda ake kira Amir Abu Fatima.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X, ta ce an samu nasarar kashe Abu Fatima ne a wani samame da dakarun Haɗin-Kai suka kai yankin Kukawa na jihar Borno.
Sojojin sun ce Abu Fatima na cikin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo, inda ta ƙuduri aniyar bai wa duk wanda ya bayar da rahoton inda za a kama shi ladan naira miliyan 100.
“Abu Fatima ya samu munanan raunuka lokacin da ake ba ta-kashi kafin mutuwarsa. An kuma kashe mataimakinsa da wasu ƙwararru kan ababen fashewa da dama har ma da sauran ƴan ta’adda da suke tare da shi,” in ji sanarwar.
Dakarun sun kuma ƙwato bindigogin AK-47 da harsasai da kuma abubuwan fashewa.
Ta ce babu jami’inta ko ɗaya da ya mutu ko ya samu rauni yayin samamen.
Wannan dai babban koma-baya ne ga jagorancin mayaƙan na Boko Haram a yankin, da kuma ƙarin ƙarfin gwiwar sojojin Najeriya wajen dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas a daidai lokacin da ake ganin dawowar ayyukan mayaƙar.

