• Home  
  • Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Rabon Shinkafar Dangote
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Rabon Shinkafar Dangote

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon tallafin shinkafa ga mutum 120000 wanda gidauniyar Aliko Dangote ta samar, kamar yadda ta sa ba, a duk shekara.

Daga: Hauwa Umar Tela
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon tallafin shinkafa ga mutum 120000 wanda gidauniyar Aliko Dangote ta samar, kamar yadda ta sa ba, a duk shekara.

Taron kaddamar da rabon tallafin shinkafar  buhu 120000 mai nauyin kilogram 10, ya gudana ne a fadar gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagoranci Haj. Mariya Aliko Dangote, wanda Hukumar Hisba ta jihar Kano zata jagoranci rabon tallafin.

Hajiya Mariya ta bayyana ƙudurin mahaifin ta na tallafawa mabuƙata, ta ce anfara kuma za’a yi tayi.
Anasa ɓangaren mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci gwamna Kano ya kaddamar da rabon tallafin tare da yin godiya ga gidauniyar Aliko Dangote bisa gudunmawar da take baai wa gwamnatin jihar Kano.

Mataimakin babban kwamandan Hisbah Dr. Mujahideen Aminudeen wanda ya jagoranci rabon tallafin da za’a yi a ƙananan hukumomi 44, yace sunyi alƙawarin yin aiki bisa gaskiya da riƙon amana.
A ƙarshe, wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin da suke ciki haɗi da godiya ga gidauniyar ta Aliko Dangote.
Taron yasamu halartar manyan mutane daga sassa daban daban a faɗin ƙasar nan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai