Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nada tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Muhammad Attahiru Jega a matsayin uba ga sabuwar Jami’ar nazarin koyar da aikin malinta ta Kano.
Kazalika Gwamnatin ta Kano, ta amince da nada Oba Dokta Moshood Olalekan Ishola Balogun Aliiwo a matsayin shugaban majalisar kula da ayyukan Jami’ar.
Kwamishinan labaran gwamnatin Kano, Malam Mohammed Garba wanda ya sanar da haka bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a ranar Lahadi, ya ce a kwanan nan ne hukumar kula da Jami’o’i ta Nijeriya wato NUC ta amince da daga likafar kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa matsayin Jami’ar nazarin koyon aikin malinta.
Gabanin zama shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shugabanci Jami’ar Bayero Kano tsawon shekaru biyar, haka kuma kafin haka, ya kwashe shekaru da dama yana koyar da ilimin kimiyyar siyasa a Jami’ar ta Bayero.
Kwamishinan ya ce sauran mambobin majalisar kula da ayyukan sabuwar Jami’ar sun hada da Dokta Muhammad Adamu Kwankwaso da Hajiya Zulaiha U.M Ahmed da Dokta Ibrahim Yakubu Wunti Dokta Halima Muhammad da kuma Alhaji Sabiu Bako.