Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin dukkanin makarantu masu zaman kansu a jihar.
Wata majiya ta ruwaito cewa an dauki matakin ne a ranar Asabar yayin wata ganawa tsakanin mammallaka makarantu masu zaman kansu da kuma gwamnatin jihar kano.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu da na sa kai, Alhaji Baba Abubakar Umar ya bayyana cewa ana bukatar dukkan makarantu masu zaman kansu su sabunta rajistarsu cikin gaggawa, saboda gwamnati za ta fara bayar da sabbin satifiket ga makarantun.
Alhaji Baba Abubakar Umar ya bayyana cewa matakin ya jaddada kudirin gwamnati na ganin cewa makarantu masu zaman kansu sun bi ka’idojin da aka gindaya musu game da gudanar da aikinsu yadda ya dace a wannan jihar nan.
Sannan an tunatar da masu makarantun alhakin da ya rataya a wuyansu na biyan haraji kashi 10 ga gwamnati.
Mai ba da shawara na musamman Alhaji Baba Abubakar Umar ya kuma tabbatar wa iyayen dalibai cewa za su ci gaba da ba su fifiko wajen kiyaye muradunsu da na ‘ya’yansu.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu reshen jihar Kano, Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka, yana mai kallon matakin a matsayin abin yabawa a fannin ilimi.