Home » Kano: Hukumar NEMA ta raba tallafi ga wadanda suka gamu da ambaliyar ruwa

Kano: Hukumar NEMA ta raba tallafi ga wadanda suka gamu da ambaliyar ruwa

by Hassan Abdu Mai Bulawus
0 comment
Kano: Hukumar NEMA ta raba tallafi ga wadanda suka gamu da ambaliyar ruwa

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya National Emergency Management Agency (NEMA) ta ƙaddamar da rarraba kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022 da kuma mabuƙata a nan jihar Kano.

Shugaban hukumar, Mustapha Ahmed-Habib, ya ce suna sa ran raba kayan ga iyalai 660,000 a faɗin Najeriya.

Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdulsalam-Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a rabon kayan ranar Asabar, ya ce za ai rabon ne ga iyalai dubu 22,678 da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar da ta gabata a Kano.

Inda  iyalai 979 za su amfana daga ƙananan hukumomi 20 na Kano, yayin da aka ware wa ƙananan hukumomin Kano Municipal da Tarauni 1,520 kowacce.

Cikin kayan abinci da aka raba akwai shinkafa, da wake, da dawa, da kayan miya, da gishiri, da kuma sinadaran ɗanɗano.

Kazalika, an raba kayayyakin noma da na inganta rayuwa kamar gidan sauro, da ledoji, da barguna, da katifu, da botikai na roba, da risho, da tukunyar girki.

Aminu Abdulsalam ya nemi waɗanda suka amfana da tallafin da kada su sayar da su, yana mai cewa an ba su ne don su inganta rayuwarsu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?