286
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da ɓullar cutar anthrax a kasar a hukumance.
Wata sanarwa da ma’aikatar Noma da Raya karkara ta yi, ta ce an kai rahoton dabbobin da ke nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar anthrax a wata gona da ke Suleja a Jihar Neja zuwa ofishin babban jami’in kula da dabbobi na Najeriya a ranar 14 ga watan nan.