Gwamnatin Sakkwato ta tallafa wa Alhazai 47 da suka ɓatar da kuɗin guzurinsu

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta tallafa wa Alhazai 47 da suka ɓatar da kuɗaɗen guzurinsu yayin gudanar da aikin Hajjin bana a Saudiyya, domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Alhazan da abin ya shafa sun karɓi tallafin da ya kai kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da suka yi asara yayin zamansu a biranen Madina da Makkah.

Da yake sa ido kan rabon tallafin, Mataimakin Amirul Hajj na jihar kuma Babban Alƙali, Alhaji Sodangi Acida, ya yaba wa Gwamna Ahmad Aliyu Sakkwato kan wannan mataki, yana mai cewa tallafin ya zo a kan gaɓa kuma zai amfani waɗanda abin ya shafa matuƙa.

Ya ce matakin ya nuna yadda gwamnatin jihar ke kula da jin daɗin al’ummarta da kuma ƙoƙarinta rage wa Alhazan wahalhalun da suka fuskanta.

“Wannan tallafi zai taimaka matuƙa wajen rage wa Alhazan matsalolin da suka shiga, kuma yana nuna damuwar gwamnati kan walwalarsu,” in ji shi.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Jin Daɗin Alhazai na 2026, Alhaji Malami Dan Isha, ya bayyana cewa dukkan Alhazai 47 da suka yi asara sun karɓi rabin kuɗaɗen da suka rasa a lokacin zamansu a biranen biyu masu tsarki.

Ya ƙara da cewa wannan tallafi ya zo ne baya ga wata kyauta da gwamnatin jihar ta bai wa dukkan Alhazan Sakkwato, inda kowannensu ya karɓi Riyal 1,000 na Saudiyya a matsayin goron Sallah.

Alhaji Malami Dan Isha ya buƙaci Alhazan da su ci gaba da yi wa Jihar Sakkwato da Najeriya addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

Post masu alaƙa

Rukunin farko na ‘yan Najeriya da aka kwashe daga Afirka ta Kudu zai isa ƙasar ranar Alhamis

An kammala shirye-shiryen tabbatar da tsaro a zaɓen cike gurbin ɗan majalissar wakilan Dawakin Kudu/Warawa a Kano.

Mutane 3 sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Najeriya