Najeriya ta yi martani kan kisan ɗan ƙasarta a Afrika ta Kudu

Gwamnatin Najeriya, ta hannun ofishin jakadancinta da ke Johannesburg, ta yi allawadai da kisan wani ɗan ƙasarta, Ibeh Chika Simon, wanda ya mutu a yayin wani samamen da ‘yansandan Afirka ta Kudu suka kai a Bellville da ke Cape Town a ranar 23 ga Yuli.

Jakadancin ya ce mutuwar tasa ta faru ne a yanayi mai cike da tambayoyi, yayin da kuma wani ɗan Najeriya, Egwabor Patrick Chuks, ya samu munanan raunuka bayan an harbe shi a wannan samame.

A wata sanarwa, ofishin jakadancin ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da yadda lamarin ya faru, yana mai zargin jami’an tsaro da amfani da matakan da suka kai ga mutuwar marigayin.

Haka kuma, ya bayyana lamarin a matsayin wani ɓangare na abin da ya kira ci gaba da kashe-kashen da ba a warware ba da kuma zargin cin zarafin baƙi a Afirka ta Kudu.

Najeriya ta buƙaci hukumomin ƙasar su gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da gaskiya tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

A nata ɓangaren, Kwamitin Ministoci kan Harkokin Hijira na Afirka ta Kudu ya ce ana ci gaba da binciken abin da ya faru.

Ministar Shari’a Afrika ta Kudu, Mmamoloko Kubayi, ta ce a yayin samamen ƴansandan, wasu mutane sun yi turjiya ga jami’an tsaron yayin da kuma wasu baƙi suka hana su gudanar da aikinsu.

Ta ce za a bayyana sakamakon binciken idan an kammala shi, tare da ƙara da cewa gwamnati na damuwa da hare-haren sintiri da ake kai wa baƙi, inda aka kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a irin waɗannan ayyuka

Post masu alaƙa

Sojoji sun ceto mutum 48 da aka sace a Zamfara

Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Zamfara

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.