Gwamnatin jihar Sokoto ta ware kuɗi domin sayo takin zamani da iri ingacce da magungunan feshin gona da sauran ayyuka, inda gwamnatin ta ce za ta kashe naira 1,652,400,000, wanda a cewarta ɗoriya ce ga manoman jihar bayan wanda ƙananan hukumomi ta raba.
An bayyana haka ne bayan taron majalisar zarwarwar jihar, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da an ba manoman kayyakin aiki a cikin lokaci domin su yi amfana da su yadda ya kamata, sannan noma ya musu sauƙi.
Haka kuma gwamnatin jihar ta ware naira 1,609,146,000 domin sayo baburar da za a raba wa ma’aikata a matsayin lamuni mai sauƙi.
“Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da bai wa ma’aikatan jihar baburar ne domin cika alƙawarin da ya ɗauki a jawabinsa na ranar ma’aikata a Sokoto,” kamar yadd sanarwar ta bayyana.
Haka kuma gwamnatin jihar ta amince da gina asibitoci ƙanana a garuruwan Majemar Korino da Tudun Wada da ke ƙaramar hukumar Sokoto ta Kudu.