Yan bindiga sun lafta wa manoma sabbin haraji a Sakkwato
Mazauna akalla ƙauyuka 26 a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato sun fara tara kuɗi domin biyan sabon harajin da ‘yan bindiga suka ƙaƙaba musu kafin noma gonakinsu a daminar bana. Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan sun yi barazanar yin garkuwa ko halaka duk wanda suka gani yana aikin gona […]