Gwamnatin Tarayya ta aike wa jihar Kwara manyan motoci maƙare da shinkafa

Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da karɓar manyan motoci maƙare da buhunhunan shinkafa daga gwamnatin Najeriya.

A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce, Buhunhunan shinkafar 1,200 da gwamnatin ta bayar, wani ɓangare ne na rage raɗaɗin tsadar rayuwar da cire tallafin man fetur yasanya al’umar ƙasar nan.

A kwanakin baya ne dai, shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu, ya bayar da umurnin rarrabawa jihohin ƙasar nan abinci, domin sauƙaƙawa jama’a matsalar abinci.

Gwamnatin jihar Kwara ta ce tana sa ran ƙarasowar ƙarin manyan motoci uku na shinkafar kamar yadda Sakataren labaran jihar, Rafi’u Ajakaye, ya tabbatar.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro