Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikatan ɓangaren shari’ar ƙasar da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki na sani ba sabo wajen tabbatar da adalci, inda ya yi gargaɗin cewa ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar waɗanda aka ba amanar tabbatar da hukunci sun fara cin amana da tauye haƙƙin mai haƙƙi.
Tinubu ya bayyana haka ne a taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar hukumar shari’a ta Najeriya suka shirya a Abuja.
Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, ya ce gwamnatinsu ba ta sa baki a harkokin shari’a, “mun ba ɓangaren shari’a da hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba,” in ji shi.
Da yake bayyana irin nasarar da suka samu wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, Shettima ya ce EFCC ta ƙwato samu nasarar ƙwato dukiya da ta haura naira biliyan 500 a cikin shekara biyu.
“A cikin shekara biyu na wannan gwamnatin, EFCC ta samu nasarar gabatar da sama da mutum 7000 a kotu, sannan ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500.”
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen da aka ƙwato ana karkatar da su ne wajen amfanar da al’umma, musamman wajen aiwatar da shirye-shiryen walwalar al’umma kamar bashin ɗalibai da sauransu.