Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙi da ta’addanci a yankin.
Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo babban birnin Jihar Taraba.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin, don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon gwamnatin tarayya da hukumar NEDC domin gyara manyan gadojin da ruwa ya lalata.
- Kasa Hada Malamai A Dandamali Daya Ke Kawo Baraka: Dakta Sa’id Dukawa.
- An Kama Direban Mota Da Jabun Kuɗin A Oyo
Haka kuma, sun koka kan tsadar kayan aikin gona da suka ce na iya janyo ƙarancin amfanin gona a shekara mai zuwa.
Saboda haka, sun buƙaci a ƙara bai wa manoma tallafi da kuma bunƙasa shirin noman rani.
Bayan haka, gwamnonin sun amince da gudanar da bikin baje kolin kasuwanci na Arewa maso Gabas a Maiduguri a watan Disamban 2025, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar NECCIMA.

