• Home  
  • Uba Sani Yaro Na Ne A Siyasa Ba Aboki Ba – El-Rufi
- Babban Labari - Labarai

Uba Sani Yaro Na Ne A Siyasa Ba Aboki Ba – El-Rufi

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Gwamnan Kaduna, Uba Sani bai abokinsa ba ne, kawai yaronsa ne na siyasa. El-Rufai ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ƙara da cewa yanzu ba sa magana da gwamnan mai ci, “saboda duk wajen da na bari bayan na gama aikina, ba na […]

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Gwamnan Kaduna, Uba Sani bai abokinsa ba ne, kawai yaronsa ne na siyasa.

El-Rufai ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ƙara da cewa yanzu ba sa magana da gwamnan mai ci, “saboda duk wajen da na bari bayan na gama aikina, ba na komawa sai dai idan an neme ni.”

“Ba ɓatawa muka yi da gwamnan ba, dama ba abokina ba ne. Yarona ne a siyasa, wanda na ɗaura a hanya. Don haka ba wai ɓatawa muka yi ba,” in ji shi, sannan ya ƙara da tabbatar da cewa yanzu ba ya magana da gwamnan na yanzu.

Tsohon ministan na Abuja ya ce yana alfahari da zama silar ɗaukakar mutane da dama, “wasu ma sun wuce matakin da na taka. Ina jin daɗi da alfahari da haka.”

Sai dai ya ƙara da cewa taimakon mutum ya samu nasara ba zai hana shi sukarsa, “idan mutum ya kauce hanya, ya daina yin abin da ya dace, shin don na taimaka wajen samun nasararsa, sai ya zama dole ba zan yi magana ba? haka ƙasar ta koma a yanzu?”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000