Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da harin da aka kai Maiduguri 

Kungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF) ta yi Allah-wadai da mummunan harin ƙunar-baƙin-wake da ya auku a yammacin jiya na Litinin a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Aminiya ta ruwaito yadda aka samu tashin bama-bamai kashi uku a kusan lokaci guda a Asibitin Koyarwa na Maiduguri da babbar kasuwar nan ta Monday Market da kuma yankin Gidan Waya da Aika Saƙonni, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya fitar, ya bayyana matuƙar alhini kan harin, tare da miƙa ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Borno musamman iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Ya ce babu shakka an kai harin ne da nufin jefa tsoro a zukatan jama’a da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

“Wannan mummunan aiki cin zarafi ne ga bil’adama baki ɗaya, kuma dole ne a yi Allah-wadai da shi da kakkausar murya,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma jajanta wa waɗanda suka jikkata, yana mai yi musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa, tare da yaba wa jami’an agaji da hukumomin tsaro kan gaggauta ɗaukar mataki.

Ya jaddada ƙudurin gwamnonin Arewa na ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro domin kawo ƙarshen ta’addanci da sauran miyagun laifuka.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin taimakawa bincike.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, tare da kira ga hukumomi da su kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda