• Home  
  • Hajj 2025: Maniyyata Sama Da 2000 Sun Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
- Babban Labari - Labarai

Hajj 2025: Maniyyata Sama Da 2000 Sun Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa ranar misalin ƙarfe 8:02 ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki. Hukumar ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami’i guda ɗaya. Wannan dai shi ne cikamakin jirgi na biyar […]

Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa ranar misalin ƙarfe 8:02 ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumar ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami’i guda ɗaya.

Wannan dai shi ne cikamakin jirgi na biyar da suka yi jigilar maniyyatan daga ranar da aka ƙaddamar da jigilar wato ranar Juma’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000