Home » Gaskiyar Lamari: Gidan Yarin Goron Dutse.

Gaskiyar Lamari: Gidan Yarin Goron Dutse.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

 

Biyo bayan zargin yin lalata da maza a gidan kurkun Goron Dutse Kano, Gidan Telebijin da Radio na Muhasa tare da hadin gwiwar rundunar  kishin Kano wato RKK, sun kai ziyarar ganewa idonsu don binciken abinda ke faruwa.

Ziyarar ta kunshi yan jarida da lauyoyi wadanda suka duba dakunan daurarrun da kuma abincin da ake basu kowacce rana , harma da kulawar da ake basu idan basu da lafiya tare tantance abunda da suka gani dangane da zargin da ake yi.

Hadakar yan jaridun da kuma lauyoyin sun yi wa wasu daurarrun tambayoyi, inda suka tabbatar da cewa ba a aikata abunda ake zargi ba.

Wasu daga cikin daurarrun sun ce iya zamansu a gidan ba suga wurin da ake aikata hakan ba, kuma basu taba samun labari makamancin haka ba kawai karyace da aka shiryawa hukumar gidan yarin.

Shugaban rundunar kishin Kano, Janar Ibrahim Sani Yakasai mai ritaya, wanda Barista Sunusi Salisu Aliyu, ya wakilta ya bayyana cewa sunje ne doming ani da idonsu don tantance zargin da wani mutum yayi na cewa ana lalata da maza a gidan.

Barista Sunusi Aliyu, ya kara da cewa yanzu sun tabbatar da cewa maganar da yadawa karya ba a aikata irin wannan laifi a gidan yarin Goron Dutse.

Ya kuma yi kira ga kungiyoyin addinin musulinci da su shigo su dinga tallafawa daurarru da kayan bukatun yau da kullum wajen gyara musu makwanci da kuma ruwan sha.

Anata bangare Barista Badi’a Abdullahi Mu’az, ta bayyana cewa duk da zabo musu wadanda suka yiwa tambayoyin aka yi akwai bukatar a inganta abincinsu da kuma bangaren kula da lafiyarsu, amma dai taji dadi sosai sakamakon yadda aka samu chanji sakamakon baya, kuma jami’an gidan yarin sune suka yi karo-karon jini har Leda biyar aka karawa wadanda basu da lafiya.

Barista Badi’a, ta kara da cewa wasu daga cikin wadanda suka tambayoyin sunce suna koshi, amma kakakin gidan yarin Kano Musbahu Lawan ya ce ba a koshi yafi kawai akeyi domin mutum ba a gida yake ba.

Kakakin hukumar gidan yarin kano, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa , sun godewa Allah game da abunda daurarrun suka bayyana da kansu, kuma sun tabbatar da cewa ba a aikata irin laifin da ake zargi.

A karshe rundunar kishin Kano, ta yi fatan masu hannu da shuni za su  sanya hannunsu wajen taimakawa dararrun da kayan bukatun rayuwa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?