Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya amince da naɗa Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji (Dr) Hamim Muhammad Nuhu Sanusi, a matsayin Amirul Hajjin Jihar Jigawa kuma shugaban tawagar gwamnatin jihar don aikin Hajjin shekarar 2026 mai zuwa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa (SSG), Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu.
Baya ga Amirul Hajji, Gwamnan ya kuma amince da naɗa Malam Umaru Nasarawa da Alhaji Kabiru Ali Kachallan Dutse a matsayin mambobin tawagar Amirul Hajji. Haka kuma, an naɗa wakilin Sarkin Gumel, Imam Nura Salisu Abubakar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kazaure, a cikin tawagar.
Sanarwar ta bayyana cewa an yi waɗannan naɗe-naɗen ne bisa la’akari da kyakkyawan tarihin ayyukansu na jajircewa, ƙwazo, kishin ƙasa, amana da tsoron Allah.
Yayin taya sabbin waɗanda aka naɗa murna, Sakataren Gwamnatin Jihar ya buƙace su da su ci gaba da nuna waɗannan kyawawan halaye a yayin da suke gudanar da muhimman nauyikan da aka ɗora musu, domin ƙara tabbatar da amincewar da gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa suka ba su.
A cewar sanarwar, ana sa ran tawagar Amirul Hajji za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, tare da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a matakin Jiha, Tarayya da kuma ƙasa da ƙasa, domin tabbatar da ingantaccen da kuma nagartaccen gudanar da aikin Hajji.
Dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

