Home » Hakimin Kuraye Ya Faɗi Dalilinsa Na Daura Auren Mai HIV

Hakimin Kuraye Ya Faɗi Dalilinsa Na Daura Auren Mai HIV

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Hakimin  Kuraye da ke ƙaramar hukumar Charanchi a jihar Katsina,  Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu, ya magantu game da tuɓe shi da sarautarsa da aka yi.

A jiya ne majiyarmu ta rawaito yadda masarautar Katsina ta fitar da korar Sarkin Kurayen Katsina bayan samun umarni daga gwamnatin jihar ta hannun sakataren jihar.
Sai dai da ya yake bayyana yadda ya al’amarin ya faru, ya ce tabbas waɗancan mutane biyun, wato ma’auratan, sun zo wajensa domin shigewa gaba a lamarin aurensu kasancewarsa wakilin ɗaya daga cikinsu.

Ya ce akwai doka da ta hana cin zarafin masu cuta mai karya garkuwar jiki, HIV, domin haka, ya kai su zuwa ga cibiyar likitoci masu ba da shawara da kuma hukumar kula da cutar AIDS.

Inda aka ba su shawara a kan auren, sannan suka yi alkawarin kiyaye ƙa’idojin yin hakan.

A cewarsa a duk sand mutum ɗaya ke da cutar ko duka biyun, to domin gujewa muzantawa, ana jingine batun wasu shaidun gwaje-gwaje ne.

Ya kuma ba da tabbacin cewa dukkan hujjoji – da suka haɗa da takardar yarjejeniya daga ɓangarorin biyu da magungunan da aka umarce su da amfani da shi da yarjejeniyar kiyaye bayanansu – an miƙa su ga gwamnatin jihar.

A karshe, ya ce al’umma ne za su yi masa adalci a kan matakin da aka ɗauka a kan sa na rashin adalci.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?