Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta ce ta bankado shirin da wasu ke yi don bata sunanta da na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sakamakon tsare Godwin Emefiele, shugaban babban bankin kasar da aka dakatar daga aiki.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Asabar ta ce jami’anta sun gano cewa wasu mutane da kungiyoyi na shirin gudanar da zanga-zanga a wasu sasan kasar da zummar “bata sunan” hukumar da gwamnati bisa “dakatarwa da kuma yin bincike kan Mr Godwin Emefiele.
Sanarwar na cewa wadannan kungiyoyi za su taru a sassa daban-daban na Abuja da Lagos a makonni masu zuwa dauke da kwalaye masu rubutun da ke nuna gwamnati a matsayin mara kyau sannan su yi kira da a saki Emefiele nan take.
A makon jiya ne wata kotu ta umarci DSS ta bai wa iyalan Emefiele damar ganawa da shi, amma a sanarwar tata hukumar ta ce tuni ta bai wa “iyalan Emefiele, likitoci da duk mutanen da suka dace damar ganawa da shi, tun ma ranar da aka tsare shi, kafin kotu ta umarci a yi hakan.