‘Yan sandan farin kaya (DSS) daga yankin Arewa maso Gabashin ƙasar nan ta buƙaci gwamnonin yankin da su mayar da hankali wajen rabon kayan tallafin gwamnatin tarayya domin ɗorewar zaman lafiya a yankin.
Wannan shawara na zuwa ne a bayan wani taro da darektocin hukumar ta DSS na jihohi shida da ke yankin suka gudanar a a hedikwatar hukumar a birnin Maiduguri ta jihar Borno.
Manufar taron dai shi ne lalubo hanyar samun bayanan sirri da irin rawar da hakan zai yi wajen yaƙi da ta’addanci a yankin.
Bayan kammala taron, Darektocin, a ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Abdullahi Hassan, sun ziyarci gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, domin sanar da shi matsayar da suka cimma.
Gwamna Zulum wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Arewa maso Gabas, ya miƙa godiyarsa ga darektocin, sannan ya yi alƙawarin yin aiki tare da takwarorinsa domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma yi alƙwarin tuntuɓar gwamnonin jihohin Yobe, Adamawa, Taraba, Gombe da Bauchi domin tabbatar da cewa an yi rabon kayan tallafin yadda ya dace ga talakawa.
Gwamnatin tarayyar dai ta bayyana shirinta na raba wa jihohin ƙasar nan da birnin tarayya Abuja, tallafin Naira biliyan 5 domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan.