Hukumar da ke yaƙi da yi wa arziƙin ƙasa ta’annati EFCC ta ce ba ta neman tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ruwa a jallo.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter EFCC ta ce ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jan hankalinta da aka yi kan rahoton wata jarida da ta wallafa a ranar Lahadi 18 ga watan Yunin nan da muke ciki da ke cewa tana neman Matawalle ruwa a jallo. EFCC ta ce rahoton ba daidai ba ne, ya zuwa yanzu ba ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ba, ko neman DSS ta kama mata shi.
Sanarwar ta ƙara da cewa Hukumar na da tsarin da take bi wajen ayyana mutum a matsayin wanda take nema, kuma tana da hanyoyin da take bi ta sanar da mutane tana neman shi, ba ta hanyar amfani da majiyoyin bogi ba.
A baya-bayan nan dai an yi samun takun saka tsakanin tsohon gwamnan na jihar Zamafar da hukumar ta EFCC, inda Matawallen ya zargi tsohon shugaban Hukumar Abdurrasheed Bawa da tafka almundahana iri-iri.