Hukumar Gidan Yari A Kano Sun Musanta Zargin Yin Lalata Da Maza

Hukumar gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya reshen jihar kano, ta musanta zargin da wani matashi mai suna, Shehu Adamu, ya yi da  cewa ana lalata da maza a gidan yarin Goron Dutse, kuma hakan ya sanya mutane sama da 200 basa iya zama har tsutsotsi suke fitowa daga mazaunansu.

Kakakin hukumar gidan ajiya na jihar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma ba za su lamunci wannan cin zarafi ba , domin labarin karya ne kuma za su dauki matakin shari’a akansa da kuma wadanda suka yada ba tare da sun bincika ba.

Musbahu Lawan, ya kara da cewa matashin bai taba zama a gidan yarin Goron Dutse ba , amma ya taba zama a gidan yarin Kurmawa, kuma watanni hudu kachal ya yi, ba kamar yadda ya bayyana ba cewa ya shafe shekaru 9 a gidan ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan fitar wani sautin murya da aka yada a shafukan sada zumunta, inda matashin mai suna Shehu Adamu, ya yi zargin cewa ana lalata maza a gidan yarin Goron Dutse.

An jiyo matshin na cewa ‘’ a halin da ake ciki daman dai neman maza a kurku munsan tsohon laifi ne, to amma abunda yake faruwa kamar a kirashi da fyade, tunda ana amfani da raunin dan adam ta hanyar a bashi Magi Dunkuli, garin kwaki a hannu to ana amfani da wannan abubuwa na lalata yara musamman yan shekara 18, 19 da 20 ta hanyar neman, wasu ma yanzu basa iya zama saboda nemansu da ake yi ta baya wanda takai a yanzu akwai sama da mutane sama da 200 wadanda basa iya zama da bayansu saboda tsutsotsi ne suke fitowa ta bayansu.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano , ta hannun hukumar hisbah ta jihar Kano ta ziyarci gidan gyaran halin da ake zargin ana lalata da maza , inda hukumar ta bincika kuma ta tabbatar da cewa labarin kirkirarsa aka yi kuma karya ce tsagoronta wadda aka kitsa.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar hisbah na jihar Kano, Dr. Mujahiddin Aminuddin , ya bayyana cewa , wannan abun bakin ciki da aka yada ne ya sanya gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya basu umarnin bincikawa kuma sun gano cewar wanda ya kitsa wannan labarin ya saba cutar al’umma don lalata sunan Kano da shari’a.

Dr. Mujahiddin Aminuddin

‘’ mun zo mun bincika abunda ya fada ko kusa ba a yi karya yi wa hukumar gidan yarin cewar’’ Dr. Mujahiddin Aminuddin ‘’.

Ya kara da cewa bisa abinda suka bincika za su dauki matakin sanya kafar wando daya akan wanda ya yada abin.

Dr. Mujahidin ya yi kira ga al’umma idan sunga wani abu da ake aikatawa na ba daidai bas ubi hanyoyin da yakamata don sanarwa amma a dinga fadar abu na gaskiya.

Haka zalika ya kalubalanci jama’a da cewa a kwanakin baya daurarrun da suke gidan sun yi saukar karatun alkur’ani mai girma amma babu wanda ya yada, ko sana’o’in da suke koya amma anzo ana yada sharri akan abunda babu tabbaci akansa.

Kakakin Hukumar gidan yarin Kano, ya ce a baya ma hukumar hisbah ta taba biya masa kudin tara naira dubu talatin kan sabanin da suka samu da wani mai gidansa, kuma gwamnatin tarayya tana samar da abinci mai kyau ga daurarrun.

Rahotanni na cewa Shehu Adamu yana amsa sunaye da dama, kamar Usman Shehu, Habu Ahmed , Aliyu daidai sauransu.

Kaza lika kuma ana zarginsa a baya ya taba kwashe kayan tsohuwar matarsa sannan ya siyar da su, kuma ya yaudari mutane da dama ta hanyar cewa ya musulinta tare da nema masa sana’a amma aka nemi shi aka rasa bayan yunkurin damfarar da ya yi wa wasu mutane da hakansa bai cimma ruwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *