• Home  
  • Sheik Bala Lau Ya Kai Ziyara Fadar Sarkin Hadejia
- Babban Labari - Labarai

Sheik Bala Lau Ya Kai Ziyara Fadar Sarkin Hadejia

Daga: Muhammad Inuwa Ibrahim Shugaban kungiyar JIBWIS na kasa, Sheik Dr. Abdullahi Bala Lau, ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Hadejia, Dr. Abubakar Adamu Maje CON, a jiya juma’a. Kamfanin Meta Ya Yi Rashin Nasara A Kotu Kan Karya Dokoki A Nijeriya Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Sabon Shugaban Gidan Gyaran Hali Ya Mayar Da Hankali […]

Daga: Muhammad Inuwa Ibrahim

Shugaban kungiyar JIBWIS na kasa, Sheik Dr. Abdullahi Bala Lau, ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Hadejia, Dr. Abubakar Adamu Maje CON, a jiya juma’a.

Wannan ne karo na uku da kungiyar Izila ta kasa takai irin wannan ziyarar fadar sarkin Hadejia don yin da’awa sakamakon kawo babbar jami’ar musulinci ta duniya Assalam Global University dake Hadejia a jihar Jigawa.

Cikin wadanda suka yiwa, Bala Lau, rakiya sun hada da skaataren kungiyar, Sheik Muhammed Kabiru Haruna Gombe da kuma sauran manyan malamai dake fadin Nijeriya.

A wajabinsa Shiek Abdullahi Bala Lau, yayi fatan jami’ar zata kawo sauye-sauye masu yawa ga al’ummar musulmin duniya baki daya.

Mai martaba sarkin Hadejia, Dr. Abubakar Adamu Maje CON,ya godewa musu bisa wannan ziyara da suka kai masa har fadarsa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai