A ranar 5 ga watan Mayu 2005 marigayi Umar Musa Yar’adu’a ya rasu, bayan ya yi fama da dogaruwar jinya, wanda yana daga cikin daidaikun zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da talakawan kasar ke kewar su, saboda kyakkyawan kamun ludayin gwamnatinsa kuma a ranar 5 ga watan mayu 2025 ya cika shekaru 15 da rasuwa.
Sai dai kuma an lura cewa yawancin shugabannin da suka fi samun irin wannan yabo daga talakawan Najeriya, ba su fiye yin tsawon rai ba a kan mulki .
Zuwa yanzu, shugabannin Najeriya huɗu ne suka mutu a kan mulki, kuma dukkansu daga yankin Arewa.
Biyu daga cikinsu zaɓaɓɓu ne a karkashin tsarin dimokuradiyya da suka hada da Marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, Fira Ministan kasar na farko, sai kuma Marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’adua.
Ragowar biyu kuma shugabannin mulkin soja ne — Janar Murtala Ramat Muhammad da kuma Janar Sani Abacha, waɗanda su ma suke shan ya yabo, duk kuwa da yadda ake wa gwamnatocin soji kallon masu takalmin karfe.
A ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010 Najeriya ta girgiza da labarin rasuwar shugaban kasarta, Alhaji Umaru Musa ‘Yar’Adua bayan fama da jinya.
Tun kafin zamansa shugaban a ranar 29 ga watan Mayun 2007, an yi masa dashen koda, lamarin da ya zama abin ce-ce-kuce a lokacin mulkinsa.
- Gwamnatin Kano Tare Da Hukumar Gidan Gyaran Hali Sun Musanta Zargin Yin Lalata Da Maza A Kano
- Yan Sandan Nijeriya Sun Kubutar Da Yan Kasar Ghana Da Aka Yi Garkuwa Da Su
A watan Satumban 2009 ya tafi kasar Saudiyya domin duba lafiyarsa, daga bisani aka sanar cewa yana fama da ciwon zuciya.
Dadewarsa yana jinya a kasar har ya mika mulki ga mataimakinsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa ta haifar da rudani inda a watan Fabrairun 2010 Majalisar Dokokin Najeriya ta yi amfani da karfinta ta ayyana mataimakinsa, Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin Shugaban Kasa.
A ranar 24 ga watan Fabarairu aka dawo da shi gida, amma Mukaddashin Shugaban kasa ya ci gaba da jan ragamar gwamnati.
Bayan watanni biyu, a ranar 5 ga watan Mayu Allah Ya yi masa cikawa, wanda haka ya ba damar rantsar da Jonathan a matsayin shugaban kasa.
Duk da rashin lafiyar Shugaba Yar’Adua ya samu farin jini a wurin al’ummar Najeriya musamman saboda manufofin gwamnatinsa 7 point Agenda, wadda ta mayar da hankali wajen inganta makamashi da wadata kasa da abinci da samar da arziki da inganta ilimi da tsaro da sufuri da mallakar kasa.
Ya yi zarra a dabi’arsa ta bin doka inda ya zama shugaban kasa na farko da ya bayyana kadarorinsa ga al’ummar kasa.
Uwa uba ya ba da umarnin sakin kudaden Gwamnatin Jihar Legas da gwamnatin Obasanjo ta ki saki daga Asusun Gwamnatin Tarayya
Kazalika a zamaninsa, duk da takunkumin da manyan kasashe suka kakaba wa Najeriya, amma ya rage hauhawar farashin kayayyaki a cikin gida, da kuma basukan da ake bin Najeriya a kashen waje daga dala biliyan 36 zuwa biliyan 27. Ya ninninka yawan kudaden da ke asusun ajiyar kasashen waje na kasar daga dala miliyan 494 zuwa biliyan 9.6 sannan ya daidaita farashin canjin dala na tsawon lokaci a kan N80.
Gwamnatinsa ya murkushe masu tayar da kayar baya a cikin gida da kuma barazanar kasashen waje, sannan ta kama tare da tatsar wasu manyan mutane da suka durkusar da wasu bankunan kasuwanci.

