Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kubutar da wasu yan mata biyu da ake zargin wani mutum ya yi yunkurin fitar da su zuwa ƙasar Saliyo don yin aikatau ko neman kuɗi ba bisa ka’ida ba.
Mukaddashin babban kwamandan hisba na jihar Kano Dr.Mujahidden Aminuddeñ Abubakar, ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce tuni jami’ansu suka cafke wanda ake zargin bayan samun bayanan sirri.
Yan matan da aka ceto sun hada da, Zahara’u Audu, daga Zaria mai shekaru 16 da Kuma ,Kalizah Salim, yai shekaru 18 daga karamar hukumar Fagge Kano.
- An Kama Yan Bindiga 5 A Jihar Kebbi
- Kabiru Tanimu Turaki Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa
Hukumar hisbah ta ce an tura batun ga hukumomin tsaro domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu akan lamarin.
Ta kuma tabbatar da cewa za a mika yan matan ga iyayensu bayan kammala bin matakan tsaro da shari’a.
Hukumar ta yi kira ga iyaye da su sanya ido kan yayansu, tare da gujewa amincewa da duk wani tsarin aiki a kasashen ƙetare da ba shi da tsari ko ingantacciyar doka.

