Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bullo da wani sabon tsari na masauki a Madina.
Ta umarci maniyyata da cewa za su shafe kwanaki biyar ne kacal a Madina su koma Makka bayan sun ziyarci Masallacin Annabi (S.A.W) da sauran wurare masu tsarki a biranen biyu masu tsarki.
Mataimakin daraktan yada labarai da na hukumar, Alhaji Mousa Ubandawaki, ne ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa, inda ya ce wannan umarni zai fara aiki ne daga yau, 8 ga watan Yunin 2023.
Sannan ya ƙara da cewa Sabuwar manufar ta zama wajibi ne biyo bayan korafin cunkoson alhazan Nijeriya a birnin Madina.
Yana da kyau a a sani cewa a karon farko cikin dogon lokaci NAHCON ta bai wa alhazan Nijeriya dari bisa dari damar zuwa Madina.
Sanin kowa ne cewa alhazan Nijeriya na zaune ne a unguwar Markaziyya ta musamman a lokacin zamansu a Madina, matakin da ya sha yaba wa matuka.
Ubandawaki ya kara da cewa, idan ana son a dore da manufofin, to dole ne a rage adadin kwanakin mahajjata a Madina.