Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci majalisar Kan Tattalin Arzikin Kasa NEC, a karkashin Kashim Shettima, ta fito da yadda za a rage radadin cire tallafin fetur ga al’uma.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ne ya bayyana haka a jiya Laraba bayan shugaban Kasa ya zauna da manyan ‘yan kasuwan mai a fadar Aso Rock.
Abiodun wanda ya taba zama shugaban kungiyar ‘yan kasuwan na mai, ya ce ‘yan kasuwa sun nuna goyon bayan cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi.
Haka kuma rahoton ya ce ‘yan kasuwan sun yi alkawarin bada gudumuwar manyan motocin daukar mutane 50 zuwa 100 domin a taimakawa talakawa.
Sun ce Kowace mota ta kai kusan Naira miliyan 100, saboda haka za a kashe kimanin N10bn a sayen
Rahotan yayi nuni da cewar, majalisar da ke kula da tattalin arzikin za ta yi nazarin karin mafi karancin albashi.