Shugaban hukunar Kanal Hameed Ibrahim Ali mai ritaya ya bada umarnin nada CSC Maiwada bayan duba nagarta da kuma iya aikinsa shekara da shekaru a hukumar.
Maiwada dai ya taba zama kakakin hukumar na Shiyya ta biyu ta hukumar kwastam dake Kaduna ya kuma rike wannan mukami a jihar Ogun dake arewa maso yamma na tsawon shekaru.
Ya dawo shalkwatar hukumar a shekarar 2020 inda ya zama jami’in hulda dake tsakanin gidan jarida na Kwastam da jami’an kwastam a bangarorin Nijeriya.
Maiwada yayi digirinsa na farko a jami’ar Bayero da ke kano, kuma a yanzu yana da digiri na biyu guda biyu kuma yana digiri na uku a harkar jarida.