Hukumar Samar Da Ruwa Ta Jihar Bauchi Ta Samu sabbin Kayan Aikin Magance Matsalar Karancin Ruwa

 

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi

Ganin yadda ake fama da matsalar karancin ruwan Sha a cikin garin Bauchi da kewaye da kuma wasu kananan hukumomi na jihar Bauchi, Hukumar samar da ruwa ta jihar ta bayyana kokarin gwamnatin jihar Bauchi na samar da sabbin na’urorin samar da hasken rana domin tallafawa hasken lantarki na kasa don a magance matsalar da ke haifar da karancin ruwa a unguwanni da garuruwa.

Injiniya Aminu Aliyu Gital, babban Manajan hukumar samar da ruwa ta jihar Bauchi shine ya bayyana haka cikin hirarsa da manema labarai a ofishin sa da ke Water board a Bauchi.
Yadda cikin jawabinsa ya godewa Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi saboda samar da na’urorin transfoma da sabbin injina don samar da hasken lantarki a dukkan tashoshin samar da ruwa da ke cikin garin Bauchi da kewaye.

Ya ce an yi duk ayyukan da suka dace yadda a halin yanzu dukkan wuraren da suke da bututun tura ruwa za su ci gaba da samun ruwa sosai. Wuraren da ba su da layin ruwa Kuma su kara hakuri har zuwa lokacin da za a ci gaba da fadada aikin kamar yadda aka yi shekara biyar da suka wuce, saboda a kullum garin Bauchi yana kara samun sabbin unguwanni saboda shigowa da ake yi daga wasu garuruwa masu fama da rashin zaman lafiya.
Injiniya Aminu Aliyu Gital ya ce shekaru biyar kenan aka yi aikin fadada hanyoyin adana ruwan da kuma dasa sabbin bututai da sauran kayan aiki irin na zamani.
Don haka ya bukaci maaikatan hukumar su inganta ayyukan su ta hanyar amfani da kayan kariya da suka dace don kiyaye aikin su da rayukan su a bakin aiki.

Don haka Aminu Aliyu Gital ya bayyana takaici game da hatsarin da wasu maaikatan hukumar hudu suka shiga a kwanakin baya har suka rasa rayuwar su a yadda aka dasa injinan tace ruwan. Don haka ya bayyana cewa hukumar ta dauki duk Wani mataimakin da ya dace don ganin Hakan bai sake faruwa ba.

Daga karshe ya roki Jama’a su rika lura da kayan da aka samar a wuraren su don ganin bata gari basu lalata ko sun sace ba. Sai mutane sun taimaki gwamnati kafin ta samu zarafin inganta rayuwar Jama’ar ta.

 

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda