Home » Hukumar Tace Fina-Finai Ta Yabawa Dakunan Taro tare da Gidajen Wasanni Bisa Bin Doka Da Oda A Kano

Hukumar Tace Fina-Finai Ta Yabawa Dakunan Taro tare da Gidajen Wasanni Bisa Bin Doka Da Oda A Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

A wani bangare na kokarin tabbatar da tsafta da kuma da’a yayin bukukuwan Sallah Babba a jihar Kano, Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Abba El-Mustapha, ta bayyana jin dadinta bisa yadda Dakunan Taro da gidajen wasannin a Kano suke bin dokokin ta, a yayin Bikin Babbar Sallah.

Kwamitin da ke da alhakin sa ido kan ayyukan wadannan guraren taro a lokacin Sallah ne ya tabbatar cewa dukkannin guraren da suka sami damar kai ziyara sun cika ka’idojin da hukumar ta shimfida a yayin bukukkuwan sallar.

Wannan bayani ya fito ne daga Shugaban Kwamitin, Alh. Lawan Hamisu Danhassan, wanda shi ne Daraktan dake lura da sashin Fina-Finai da Cigabansa a Hukumar.Ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an ci gaba da bin doka da oda, tare da daukar matakin da ya dace kan duk wanda ya karya doka batare da sani ko sabo ba.

Ya kuma bukaci masu dakunan taro da gidajen wasanni a Jahar Kano da su cigaba da bada hadin kai domin tabbatar da kiyaye al’ada tare da tarbiyar addinin musulunci.Danhassan ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Hukumar Abba El-mustapha bisa yarda da kafa kwamitin tare da dora masa alhakin sa ido tare da tabbatar da da’a a tsakanin masu zuwa gidajen wasannin tare da dakunan taron dake Jahar Kano.

Ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayanta ga aiyukan hukumar tare da amsa bukatun Hukumar akan

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?