Ɗan wasan gaban Athletic Bilbao, Iñaki Williams, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Ghana, Black Stars, ƙwallo.
Ɗan wasan haifaffen Bilbao ya koma wakiltar Ghana a shekarar 2022, bayan da ya taɓa buga wasa ɗaya a tawagar ƙasar Spain.
Ya wakilci Ghana a gasar Kofin Duniya ta 2022 da kuma ta 2026, baya ga gasar AFCON ta 2023.
A saƙon bankwana da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Williams, ya ce lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen tafiyarsa da Black Stars.
Ya bayyana cewa ya bar tawagar cikin farin ciki da alfahari, inda ya bayyana cewa tawagar ta ba shi damar sake kusantar danginsa da kuma alfaharin wakiltar ƙasarsa.
Williams ya kuma gode wa al’ummar Ghana bisa ƙauna da goyon bayan da suka nuna masa, tare da cewa zai ci gaba da mara wa Black Stars baya a duk inda yake.
Ya yi ritaya ne bayan Ghana ta fice daga gasar Kofin Duniya na 2026 a zagayen ’ya 32, bayan Colombia ta doke ta da ci ɗaya.
Yanzu Williams zai mayar da hankali kan taka leda a Athletic Bilbao, inda yake ɗaya daga cikin manyan ’yan wasan ƙungiyar.
Williams mai shekara 32 ya bayyana matakin ne a ranar Juma’a, 11 ga watan Satumba, 2026.