Shugaban Hukumar kwallon Ƙafa ta Najeriya Ibrahim Gusau ya yi murabus

Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, Ibrahim Gusau ya yi murabus daga muƙamisa.

Gusau ya shaida haka ne a yau Alhamis a shedikwatar Hukumar Kwallon Kafa ta kasar a wani taron manema labarai.

An ta suka kan yadda tawagogin Najeriya na mata da maza suka gaza ƙoƙari a ‘yan shekarun bayan nan, ciki har da gaza samun gurbi a gasar kofin duniya.

Rahotanni sun ce hukumomin Najeriya na bincike kan hukumar ta NFF game da yadda ta kashe wasu kuɗaɗe naira 17bn don biyan albashi da sauran hidimar ‘yan wasa.

A bangaren wasannin cikin gida kuma an yi zargin cewa alkalan wasa ba su samu kudadensu ba tun daga mako na 25 zuwa mako na 38, da dai sauran wasu korafe-korafe.

Post masu alaƙa

Man City ta dage kan Enzo Fernandez, Sao Paulo da West Ham na neman Vardy

Mahaifin Lionel Messi, Jorge, ya rasu yana da shekara 68

Yadda muka yi ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka a gasar Kofin Duniya – Infantino